Ganduje ya musanta zargin  cin bashin Naira biliyan 10 domin saka CCTV a Birnin Kano

Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta zargin  cin bashin Naira biliyan 10 domin saka kyamarorin tsaro na CCTV a Birnin Kano da kewaye.

Wasu gungun ƴan gwagwarmaya ƙarƙashin inuwar  Coalition of Political Analysts Forum and Good Governane [ CPFG] suka nemi gwamantin Abba Kabir Yusuf ta bincike tsohon gwamna bisa abin da ya yi da kuɗin.

Sai dai a martanin da ya fitar a Abuja, Dr Ganduje yace bai samu zarafin karɓo bashin ba saboda wata Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da shi bayan da Majalisar Dokoki ta amince masa.

A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba ya sa hannu, tsohon gwamnna ya ƙalubalanci gungun ƴan gwagwarmayar da su kawo hujjar cewa ya karɓo bashin.

Dr Ganduje ya kuma yi zargin cewa gungun ƙungiyoyin na boge ne waɗanda iyayen gidansu na siyasa ke ɗaukar nauyinsu domin ɓata masa suna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *