Zulum, ya amince da fara amfani da harabar makarantar Sakandare ta gwamnati a matsayin matsugunin wucin gadi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da fara amfani da harabar makarantar Sakandare ta gwamnati a matsayin matsugunin wucin gadi domin kaddamar da sabuwar kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya (FCE) a karamar hukumar Gwoza ta jihar.

Makaranatar ta kasance a cikin yankin wasu al’umma ne da ke cikin garin Gwoza, a karamar hukumar Gwoza.

Sabuwar cibiyar ita ce irinta ta farko a jihar Borno tun bayan da aka kirkiro jihar a shekarar 1976.

Yawancin Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja na da Jami’ar Tarayya, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da Kwalejin Ilimi ta Tarayya a jihohin, amma Jihar Borno ta kasance ba ta da Kwalejin Kimiyya da fasaha da Kwalejin Ilimi ta tarayya har sai da gwamnatin Buhari ta kafa su a kwanan baya. Gwamna Zulum, ya kaddamar da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Monguno a kwanan baya, yanzu haka ya sake kaddamar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Gwoza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *