Tinubu ya bar Nairobi bayan kammala taron AU

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya tashi daga Nairobi, babban birnin kasar Kenya, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 5 na kungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Shugaban na Najeriya ya bar Abuja ne a ranar Asabar domin ganawa da wasu shugabannin nahiyar kuma ana sa ran zai dawo kasar ranar Litinin.

A taron na AU, shugaban, a ranar Lahadi, ya ce Afirka ba za ta iya samun hadin kai da wadata ba yayin da ‘yan Afirka ke cikin kunci da talauci.

Ya jaddada haɗin kai da ƙarfin Afirka, yayin da ya yi watsi da ra’ayin sabon rikici ga nahiyar.

Har ila yau, a ranar Asabar, Tinubu ya yi kira ga shugabannin Afirka da su mutunta dimokuradiyya, bin doka da oda, da tabbatar da daidaiton siyasa.

Ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dau mataki mai tsauri kan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Tinubu ya kuma bukaci cibiyoyin sojan Afrika da jihohi su gane da kuma mutunta bukatar sabunta dimokradiyya.

An ruwaito cewa Shugaban Najeriyar, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ta shugabannin kasashe da gwamnatoci, ya ce kamata ya yi a dakile yunkurin juyin mulki a nahiyar, musamman a lokacin da ake fuskantar kalubale kamar annobar COVID-19, rashin tsaro, da sauyin yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *