Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya mika takardar murabus dinsa

Shugaban jam’iyyar (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar murabus dinsa a daren jiya.

Majiya mai tushe ta tabbatar wa da wannan jarida cewa Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a watan Maris din shekarar 2022, ya aike da takardar murabus dinsa zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja gabanin dawowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu daga taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) a Kenya.

Daya daga cikin majiyar ta ce Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya aika wasikar murabus din ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin jiya Lahadi.

Hakazalika, wata majiya ta kusa da Adamu ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa, “Shugaban na kasa ya yi murabus ne biyo bayan yunkurin da wasu mutane da ke kusa da shugaban kasa ke yi domin kunyata shi a taron jam’iyyar da za a yi gobe Talata da jibi Laraba.”

Sai dai majiyar ta musanta wani rahoto da ke cewa shugaba Tinubu ne ya bukaci Adamu ya yi murabus gabanin taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na kasa da za a yi.

Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 10 da 11 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan kwamitin ta na kasa da na NEC domin warware matsalolin da suka shafe ta da kuma rikicin da ke tsakanin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC).

Sai dai daga baya an dage tarukan tare da dage zaman zuwa ranakun Talata da kuma Laraba. Da aka tuntuɓi Adamu domin jin ta bakinsa kan wannan lamarin, ya bayyana cewa zai so a ce ya yi magana kan lamarin lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga wajen taron ƙungiyar AU daga birnin Nairobi na ƙasar Kenya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *