Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin Bola Tinubu na magance matsalar ‘yan bindiga da matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
Mataimakin ya zo Kano ne domin ta’aziyya ga iyalan marigayi Abubakar Galadanci, wanda ya rasu a ranar Juma’a.
Ya ce shugaban kasa ya kammala shirye-shiryen samar da dawwamammiyar mafita kan kalubalen tsaro da ke addabar yankin.
A cewar Shettima, nan ba da dadewa ba shugaban kasar zai bullo da wata sabuwar dabara ta yaki da ‘yan fashi da kashe-kashe a yankin, inda ya kara da cewa matakin zai hada da warware rikicin ta hanyar amfani da matakan soja da wadanda ba na soja ba.
Ya ce rikicin da ake fama da shi a yankin yana da nasaba da fatara da rashin zaman lafiya, yana mai jaddada cewa shugaban kasa ya kuduri aniyar magance shi.