Majalisar dokokin Kano ta amince da bukatar gwamna ta nada masu bada shawara na musamman

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abba Kabir-Yusuf na nadin mukamai na musamman guda 20.

Kakakin majalisar, Ismail Falgore ne ya karanta wasikar bukatar gwamnan a zauren majalisa a ranar Litinin a Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, an tattauna wasikar ne kafin majalisar ta amince da bukatar

Falgore ya ce amincewar shi ne don baiwa Gwamna Abba Kabir-Yusuf damar nada masu ba da shawara da za su taimaka masa wajen aiwatar da manufofinsa da shirye-shiryensa ga jama’a.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala) a tasa gudunmawar ya bayyana cewa nadin masu ba da shawara na musamman zai tabbatar da ci gaban jihar cikin gaggawa.

“Mai girma gwamna ya aike da bukatar nadin masu ba shi shawara na musamman guda 20 da za su taimaka masa wajen tabbatar da manufofinsa da shirye-shiryensa,” in ji shi.

Hakazalika, shugaban majalisar wanda a tare da ’yan kungiyar, suka duba wuraren da ake zubar da shara da gyaran asibitoci a cikin babban birnin, ya nuna jin dadinsa kan yadda aikin ke gudana.

A asibitin Hasiya Bayero, shugaban majalisar ya ce sun gamsu da yawan fitowar marasa lafiya, wanda hakan ya nuna yana da matukar muhimmanci ga jama’a.

Sannan ya gode wa ma’aikatan asibitin bisa jajircewar da suke yi wa bil’adama, ya kuma ba su tabbacin gwamnati na kokarin tabbatar da lafiya ga kowa da kowa a jihar.

Falgore ya kuma yaba da yadda hukumar kula da tsaftar muhalli ta gudanar da aikin share sharar da ta yi a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *