APC Ta Tabbatar Da Murabus Din Adamu

Kwamitin gudanar da ayyuka na kasa a jam’iyyar APC ya tabbatar da yin murabus din shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore a ranar Litinin din nan.

Mun ta tattaro cewa An sanar da murabus din nasu ne a ranar Litinin din nan yayin taron kwamitin NWC da Sanata Abubakar Kyari ya jagoranta.

Kyari ya kuma bayyana cewa ya karbi mukamin shugaban riko yayin da mataimakin sakatare na kasa Barista Festus Fuanter ya karbi mukamin mukaddashin sakatare.

An ruwaito cewa Sabbin shugabannin sun kuma sanar da dage taron majalisar zartaswar na kasa da aka shirya gudanarwa tun a ranar Talata da Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *