Afirka ba za ta iya samun haɗin-kai da wadata ba — Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce Afirka ba za ta iya samun haɗin-kai da wadata ba yayin da ‘yan nahiyar ke ci gaba da shiga kunci.

A cikin jawabinsa na farko a taron tsakiyar shekara na kungiyar haɗin kan Afrika karo na biyar a Kenya a jiya Lahadi, Tinubu ya tabbatar da buƙatar samun hadin kai a Afirka da watsi yiwuwar faɗa wa sabon rikici ga nahiyar.

Tinubu ya kuma yi gargaɗin cewa ba za su lamunci cin zarafin ƴan nahiyar da ake yi ba kamar kuma yadda ya faru a baya.

Ya kuma bayyana shirin karfafa rundunar haɗin gwiwa ta kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika domin dakile juyin mulki da yaki da ta’addanci a yankin.

Shugaban na Najeriya, wanda shi ne shugaban kungiyar Ecowas, ya bayyana irin ci gaban da kungiyar ta samu a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da kasuwanci da zirga-zirgar jama’a da inganta zuba jari da samar da ababen more rayuwa da tsaro da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *