Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da bukatar karbo bashin dala miliyan 800

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da bukatar karbo bashin dala miliyan 800 don amfani dasu wajen ragewa talakawa radadin cire tallafin man fetur.

Bukatar shugaban ta kasance a cikin wata wasika da Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Tinubu ya bayyana cewar za’ayi amfani da rancen ne wajen habbaka shirin samar da zaman lafiya a kasar nan.

Ya ce sabon rancen za a karbo shi ne daga Bankin Duniya.

Ya kuma bada tabbacin gwamnatin tarayya zata biya Naira 8,000 duk wata ga marasa karfi mutum miliyan 12 na tsawon watanni shida.

Ya kara da  cewar za’a  tura kudaden ne kai tsaye zuwa asusun wadanda zasu amfana da su.

Tunda farko shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta amince masa ya karbo rancen don rage radadin cire tallafin man fetur fa ya yi.

Idan za a tuna a ranar 29 ga watan Mayu 2023, Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki. Lamarin daya sanya farashin man fetur yin tashin gwauron zabi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *