Tinubu ya bar Abuja zuwa Nairobi domin halartar taron AU

Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya, inda zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka don halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 5 na kungiyar Tarayyar Afirka AU.

Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu Ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila da Dele Alake, mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru.

Tinubu zai halarci taron ne a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya da kuma sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.

Taron mai taken “Haɓakar aiwatar da yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka” zai tattaro ofishin Majalisar AU, wanda ya ƙunshi shugabannin ƙasashe da gwamnatoci daga Comoros, Botswana, Burundi da kuma Senegal, tare da shugabanni daga ƙasashe takwas na tattalin arzikin yankin.

Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *