Buni: “Mun dauki kwararan matakai na tabbatar da tsaron lafiyar masu yi wa kasa hidima a Jihar Yobe”.

Gwamna Mai Mala Buni ya ba da tabbacin tsaron dukkanin matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka tura Jihar Yobe. 

Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin bikin rantsar da sabbin matasa masu yi wa kasa hidima rukunin ‘B’ stream I na shekarar 2023 a sansanin horar da su da ke Dazigau.

An ruwaito cewa Gwamna Buni ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman kan samar da arziki da ayyukan yi, Abdullahi Bego.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai na tabbatar da tsaron lafiyar matasan a Jihar Yobe.

A nata bangaren, Ko’odinetan NYSC ta Jihar Yobe, Misis Hafsat Yerima, ta yi maraba da matasan da aka turo Yobe hidimta wa Najeriya.

“Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya yi muku jagora baki daya zuwa sansanin horarwa a nan Yobe.

“A madadin Darakta Janar na hukumar, ma’aikata da daukacin jami’an hukumar da ke aiki a Jihar Yobe, ina so in taya ku murnar kammala karatun ku na manyan makarantu daban-daban wanda ya ba ku damar shiga cikin gurbin wadanda za su yi wa kasa hidima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *