An tura masu yi wa kasa hidima 1,900 zuwa Kano

Gwamnatin jihar Kano ta baiwa masu yi wa kasa hidimar da aka tura jihar tabbacin tsaro da isassun kulawa a cikin shekarar aikinsu.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a wajen bikin rantsar da ‘yan yi wa kasa hidima sama da 1,900 2023 Batch “B” Stream One National Youth Service Corps (NYSC) a sansanin wanzar da zaman lafiya a Kussala, karamar hukumar Karaye na jihar.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilce shi, ya jaddada cewa an samar da matakan da suka dace kuma za a ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, Gwamna Abba ya bayyana yadda gwamnati ta himmatu wajen karfafa matasa da bunkasa ilimi a jihar.
‘’Ya kuma kara da cewa inganta fannin ilimi na daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin sa ta sa gaba. ”

‘’Gwamnan ya bayyana imaninsa cewa hidimar aikin wajaba na shekara daya da ‘yan kungiyar suke yi a jihar Kano zai taimaka matuka wajen cimma burin gwamnati na bunkasa ilimi.’’

‘’Ya kara musu kwarin guiwa da su tunkari wuraren aikinsu na farko da sadaukarwa tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban jihar.

Ko’odinetan NYSC na jihar, Malam Sulaiman Andy Ibrahim ya bayyana cewa a halin yanzu masu yi wa kasa hidimar suna samun horo kan harkokin shugabanci, kasuwanci, da ayyukan soja,’’ in ji sanarwar.

‘’Ya yaba wa keɓewarsu kuma ya nuna tabbacin cewa za su yi nasara a shekarar hidimarsu.’’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *