Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun samar da abinci a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al’amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.
Alake yace umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa Tinubu na tabbatar da tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.
Ya kara da cewar Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan najeriya
Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta baiwa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.