Kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta shigar kan Okorocha.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai kan tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.

Kotun ta bayyana tuhumar da EFCC ke yi mata na zamba da cin zarafi a matsayin cin zarafin tsarin shari’a.

A ranar Juma’a ne alkalin kotun mai shari’a Yusuf Halilu ya gabatar da hukuncinsa kan yadda hukumar EFCC ta kai karar tsohon gwamnan jihar Imo a babbar kotun tarayya, inda aka yanke hukunci kan tsohon gwamnan a watan Disambar 2022.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shiga gidan Okorocha da ke Maitama Abuja inda ta kama Sanatan.

Sai dai Okorocha wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress a lokacin ya zargi hukumar da yin garkuwa da shi a gidansa.

A ranar 24 ga watan Junairu, 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu kan laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden jama’a da kadarori zuwa N2.9billion akan Okorocha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *