Cire tallafin man fetur: Gwamnatin Ebonyi ta amince da Naira 10,000 a matsayin karin albashi ga ma’aikatan jihar

Gwamnatin Ebonyi ta amince da Naira 10,000 a matsayin karin albashin ma’aikatanta a wani mataki na dakile illolin cire tallafin man fetur.

Chikadibia Okpor, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya sanar da amincewar ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da aka yi ranar Juma’a a Abakaliki.

“Batun albashin ma’aikata ya taso ne da Exco, kuma za a kara Naira 10,000 a kan albashin kowane ma’aikaci a jihar domin rage tasirin cire tallafin man fetur.” Inji shi.

Dangane da batun jami’ar jihar Ebonyi, kwamishinan ya bayyana cewa gwamna Francis Nwifuru ya umarci sakatariyar gwamnatin jihar, Grace Umezuruike, da ta binciki kudaden makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *