“Ban taɓa tsammanin mambobin ECOWAS zasu zaɓe ni a matsayin shugaba ba”. — Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yace bai taɓa tsammanin mambobin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS zasu zaɓe shi a matsayin shugaba ba.

Sai dai duk da haka shugaban ƙasar yace zaɓen da akayi masa kira ne na aiki wanda ke bukatar zage dantse da aiki tuƙuru

Tinubu ya bayyana hakan ne,a lokacin daya  karɓi bakuncin jagororin majalisar dattawa karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio

Sanatocin sun kai ziyara fadar shugaban ƙasar ne domin taya shugaba Tinubu murnar zama sabon shugaban ƙungiyar ECOWAS.

Da yake jawabin, Tinubu yace matuƙar ana son Najeriya da sauran kasashen Afrika su samu cigaba wajibi ne,a rungumi tsarin demokuraɗiyya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ya fitar,yace Shugaba Tinubu yayi alkawarin ba zai bar ‘yan Najeriya suji kunya ba wajen kokarin sauke nauyin da Allah ya ɗora masa duk da kalubalen da ake fuskanta

Tunda farko, shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio yace  zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS a taron farko daya fara hallata ya nuna yarda da sauran takwarorinsa na ƙasashen Afirka suka yi masa.

Yace majalisun tarayya  zasu cigaba da marawa shugaban kasar baya domin sauke haƙƙin dake kansa da kuma cika burin inganta Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *