Matar Shugaban Kasa ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a rukunin gidaje na TradeMore da Naira dubu 250 kowannensu.

Matar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a rukunin gidaje na TradeMore dake Abuja da Naira dubu 250 kowannensu.

A ranar 23 ga watan Yunin daya gabata ne dai wata mummunar ambaliyar ruwa ta shafe kusan ilahirin gidajen dake rukunin gidajen wadanda ke unguwar Lugbe a Abuja.

Da take jawabi a karkashin shirinta mai suna Renewed Hope Initiative, Remi, wacce matar Mataimakin Shugaban Kasa, Nana Shettima ta wakilta, ta bayyana alhininta ga mutanen.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Busola Kukoyi, ya fitar ranar Alhamis, Remi tace koda yake babu tabbacin ambaliyar ba zata sake faruwa ba tunda har yanzu ana cikin damuna, amma tana fatan taimakon zai rage musu radadin da suke ciki.

Ta kara da cewar duk da cewa har yanzu tana kan aikin yi wa shirin nata rajista da gwamnati, amma ba zai yiwu ta zuba wa mutanen ido haka kawai ba.

Da yake jawabi a madadin sauran mazauna rukunin gidajen, shugaban kungiyarsu, Dokta Adewale Adenaike, ya godewa matar shugaban kasar   kan tallafin musamman a lokacin da suke cikin tsananin bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *