Kotu ta umarci DSS su gurfanar da Emefiele ko su sake shi

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gurfanar da Godwin Emiefele, dakataccen gwamnan babban bankin Kasa CBN, a kotu nan da mako guda, ko kuma a sake shi bisa beli.

Mai shari’a Hamza Muazu ne ya bayar da wannan umarni a hukuncin da ya yanke kan wata babbar kotun kare hakkin dan Adam da gwamnan bankin ya shigar, wanda aka kama a ranar 10 ga watan Yunin 2023.

Mun ta tattaro cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele tare da ba da umarnin a binciki babban bankin da ke karkashin sa.

Rahotanni sun ce rundunar ‘yan sandan sirrin ta bi sawun sa zuwa Legas, inda aka kama shi aka garzaya da shi Abuja.

Rahotanni sun ce an hana ‘yan uwansa da abokansa da kuma lauyoyinsa ziyartarsa, lamarin da ya sanya su shigar da kara domin kalubalantar kama shi da tsare shi.

Wadanda aka shigar da karar sun hada da Babban Lauyan gwamnatin tarayya; babban daraktan hukumar DSS da kuma DSS.

A cikin karar, Joseph Daudu (SAN), lauyan Emefiele, ya ce an tauye hakkin dan adam na wanda yake karewa.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta DSS, ta bakin lauyanta, I. Awo, ya nuna rashin amincewarsa, inda ya ce tsare Emefiele ya dace, saboda hukumar ta samu umarnin wata kotun Majistare don ci gaba da tsare gwamnan babban bankin har sai an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *