Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gurfanar da dakataccen Gwanan Babban Bankin kasa na CBN Godwin Emefiele a gaban kotun.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunaya ya fitar, ya ce hukumar ta gurfanar da Emefiele a gaban kotun ne domin bin umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja data bayar data umarci hukumar ta DDS da kaishi kotu domin tuhumarsa ko kuma ta sake shi.
Sanarwar ta ambato Afunaya na cewar tun shekarar 2022 ne, hukumar DSS ta nemi umarnin kotu domin tsare Emefiele don gudanar da bincike kan wasu manyan laifuka daka zarge shi da aikatawa.
A ranar Laraba ne dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sake shi.
Emefiele ne dai ya shigar da ƙarar don tabbatar da ‘yancinsa na ɗan’adam, inda yake ƙalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS take yi.
A ranar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta bada sanarwar cewa ta kama tare da tsare Godwin Emefiele, kwana guda bayan shugaban ƙasar ya dakatar da shi.
Tsohon shugaban KASA Goodluck Jonathan ne ya naɗa Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekarar 2014.
Ya cigaba da zama shugaban babban bankin na Najeriya har ƙarshen wa’adin mulki na biyu na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Sai dai wasu matakai daya ɗauka gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 ya janyo ce-ce ku-ce mai yawa a ƙasar.