Hukumar Kwastam ta karyata rahotannin dake cewa an bude dukkan iyakokin Najeriya

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastam ta karyata rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa an bude dukkan iyakokin kasar nan.

Mukaddashin shugaban hukumar ta kwastam  Wale Adeniyi shine ya bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Aso Villa.

A watan Agustan shekarar 2019 ne dai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rufe dukkanin iyakokin kasar nan a wani bangare na kokarin dakile fasa kwauri da kuma bunkasa noman shinkafa a cikin gida.

Da yake magana kan batun, Adeniyi ya ce yayin da aka sake bude wasu zababbun kan iyakokin kasar a shekarar 2022, a halin yanzu ana ci gaba da bita don tantance makasudin rufe iyakokin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *