Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya (NIWRMC) ta fara gyara dokokinta da za su ba ta damar hukunta duk wani mai amfani da ruwa ba tare da lasisi ba a kasar.
Babban Daraktan Hukumar, Magashi Bashir, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wurin bude taron yini biyu kan sharuddan lasisin amfani da ruwa a Abuja.
Ya yi gargadin illar yawaitar rijiyoyin burtsatse a Abuja.
A cewarsa, bambancin yawan rijiyoyin burtsatse na kowane mutum a cikin wani yanayi na haifar da bala’i da ba a taba ganin irinsa ba.
Ya yi nuni da bukatar daidaita duk wasu takardu da aka yi niyya wajen sauya matsayi da kuma daidaita bangaren albarkatun ruwa.
Ya kara da cewa rashin amincewa da kudirin dokar albarkatun ruwa da majalisar wakilai ta kasa ta 9 ta yi ya haifar da kalubale da dama a harkar.