Gwamnatin Kano ta kashe Naira biliyan 1.5 wajen biyan kudin rajistar dalibai 57,000 na NECO

Gwamnatin jihar Kano ta kashe Naira biliyan 1.5 wajen biyan kudin rajistar dalibai 57,000 na hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) na makarantun sakandare daban-daban na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji Ibrahim Shuaibu, sakataren yada labarai na mataimakin gwamna Alhaji Aminu Gwarzo, ya fitar a nan Kano.

Ya ce Gwamna Abba kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude jarabawar a kwalejin Rumfa da ke cikin birni.

Inda yace dama biyan wadannan kudade na daga cikin manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na sake inganta bangaren ilimi domin samun kyakykyawan sakamako.

Ya kuma bukaci daliban da suka amfana da su yi iya kokarinsu domin samun sakamako mai kyau a jarabawar domin tabbatar da makudan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen neman ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *