Gwamnatin Adamawa ta yi alkawarin magance matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Auwal Tukur ne ya bayyana haka a wajen wata liyafar karrama tsohon ministan babban birnin tarayya, Malam Mohammed Bello da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Yola, Dr Edga Amos.

A cewarsa, ruwa yana da mahimmanci ga rayuwar dan adam, ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakan inganta samar da ruwan sha a babban birnin Yola.

Ya ce gwamnatin Fintiri ta ba da kyauta ga shirye-shiryen da za su hanzarta bin diddigin ci gaban bil’adama da zamantakewa don ci gaba mai dorewa a jihar.

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya bayyana cewa shirin bayar da tallafi ga al’ummar jihar na nan tafe domim rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

rahotanni na cewar gwamnan na kuma duba yiwuwar rage kwanaki da lokutan zuwa aiki a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar a karshen mako,gwaman Adeleke ya ɗauki wannan alƙawarin ne ga al’ummar jihar a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a birnin Osogbo.

Bayan cire tallafin man fetur da aka yi, wasu jihohi da suka haɗa da Kwara da Edo, sun ɗauki matakai domin rage raɗaɗin ƙarin kuɗin ababen hawa ga ma’aikatansu.

Adeleke ya bayyana cewa tallafin zai rage wahalar da cire tallafin man fetur ya janyo, inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki bisa manufofin jam’iyyar da alƙawuran da ya ɗauka lokacin zaɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *