ECOWAS tace tana goyon bayan kokarin Tinubu na nufin mayar da matsayin nahiyar Afirka katafariya.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS tace tana goyon bayan kokarin shugaba Bola Tinubu na nufin mayar da matsayin nahiyar Afirka katafariya.

Shugaban kasar Guinea-Buissau kuma shugaban ECOWAS, Umaro Sissoco Embalo, ya bayyana haka a wata ziyarar sirri daya kaiwa shugaban kasa Bola Ahmad  Tinubu a ranar Asabar a jihar Legas.

Ya ce matakan tattalin arziki da aka dauka kawo yanzu baza su amfanar da Najeriya kadai ba, harma da yammacin Afirka baki daya.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan ziyarar, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru Dele Alake ya ce ziyarar ta sirri ce.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas da Alake da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *