Al Makura: “Kamata yayi mutane su yabawa NAHCON ba adinga zaginta ba”

Sakataren din din din na ma’aikatar kula da jin dadin Alhazai ta Jahar Nasarawa Mallam Idris Ahmed Al Makura ya bayyana cewar kamata yayi adinga yabon Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa

NAHCON inda ya nuna cewar suna matukar kokarin ganin mahajjatan Najeriya sun samu walwalar gudanar da aikinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali

Mallam Idris Al Makura yayin wata ganawa da manema labarai tace ta yi da shi ta wayar tarho ya nuna matukar bacin ransa akan abinda da wasu suka kira kasawar hukumar wajen kula da walwalarsu

Nayi matukar mamakin jin cewa wasu da ba su san iya aikin da NAHCON keyi ba suke fadin cewar wai sun kasa cika musu alkawuran da suka daukar masu na kula da jin dadinsu

Dangane da rashin samun tantin kwana da wasu mahajjatan Najeriya suka yi wannan ba kasawar NAHCON bane

Domin Samar da tanti ga mahajjata wannan ba aikinsu bane aikin wata hukumar ce a Saudi Arabia da ake kira Mutawwif

Sune keda alhakin bayar da wajen kwana abinci da sauran bukatun da mahajjata ka iya bukata yayin gudanar da wannan ibada mai matukar  muhimmanci

Hukumar jin dadi da walwalar Alhazai ta Najeriya wadda Zikrullah Kunle Hassan yake Jagoranta idan har baa Yaba mata ba to kuma bai kamata a dinga kebewa gefe guda ana zaginta ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *