IPMAN ta karyata labarin da ake yadawa na cewa man fetur zai kai N700 kan kowacce lita

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa  (IPMAN), ta karyata labarin da ake yadawa na cewa man fetur zai kai N700 kan kowacce lita.

Shugaban kungiyar na shiyyar Kudu maso Yamma,  Dele Tajudeen ne ya bayyana hakan a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Ibadan.

Ya kuma roki jama’a da suyi watsi da labarin sannan su daina rige-rigen sayen man suna boyewa.

Yace farashin da ake sayarwa a yanzu shine mafi kololuwa, kuma ba za’a sayar dashi sama da hakan ba.

Dele Tajudden ya kuma jinjinawa Shugaban Kasa Bola Tinubu saboda cire tallafin man fetur din da ya yi.Ya kara da  cewar dan karin da aka samu a ’yan kwanakin nan anyi ne saboda karin kudin dakon man, amma mutane su tabbatar da cewar ba za’a  kara kudin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *