INEC: Nan ba da jimawa ba za mu dauki mataki kan dakataccen REC na Adamawa

Hukumar zabe ta Kasa (INEC) ta ce nan ba da dadewa ba za ta dauki mataki kan dakataccen kwamishinan zabe na jihar Adamawa REC, Hudu Ari.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa INEC, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels cikin shirin Politics Today.

Mun tattaro cewa Ari ya jawo cece-kuce a lokacin da ya bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.

Ya bayyana Sanata Aisha Dahiru Binnani a matsayin wacce ta lashe zaben ba bisa ka’ida ba.

Bayan faruwar lamarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a binciki duk jami’an da ke da hannu a wannan aika-aika.

“A game da batun REC na Adamawa, kun san cewa (tsohon) Shugaba Kasa Buhari ya dakatar da shi kafin ya bar ofis kuma ‘yan sanda sun gayyace shi don bayyana abin da ya faru,” in ji Okoye yayin hirar.

Ina sane da cewa ‘yan sanda sun kammala bincike. Nan da ‘yan makonni masu zuwa za a sanar da Najeriya abin da ya faru.

“A bisa doka, ya kamata INEC ta tuhume shi.

“Akwai wata mu’amala tsakanin ‘yan sandan Najeriya da INEC. An sanar da hukumar wasu matakai da tsare-tsare. Nan ba da jimawa ba hukumar za ta dauki mataki kan dakataccen REC,” ya kara da cewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *