“Ban hana Tinubu binciken jami’an gwamnatina ba” – Buhari

Tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace bai hana sabon shugaban ƙasa Bola Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba.

Cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami’an gwamnatinsa, labarai ne na ƙanzon-kurege.

Gabanin babbar sallah ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke Landan lokacin wata ziyarar ta ƙashin ƙai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin kuɗi na duniya da ya halarta a birnin Paris.

To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a ɗakin da suka gana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *