An umarci duk sojan da ke gaban sababbin hafsun sojojin ya yi murabus

Hedikwatar tsaro ta bada umarni ga duk sojan da ke gaban sababbin hafsun sojojin da aka nada, ya yi murabus ba tare da wani bata lokaci ba.

Hedikwatar da ke babban birnin tarayya na Abuja ta bada wa’adi zuwa Litinin domin manyan sojojin su yi ritaya da kan su.

Manjo Janar Y. Yahaya ya fitar da wannan sanarwa a madadin shugaban hafun tsaro na kasa. Takardar ta fito ne tun a ranar Litinin, 26 ga Yuni 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *