Ma’aikata a jihar Benue sun karbi albashin su na wannan watan A karon farko cikin watanni 7

A karon farko cikin watanni bakwai, Ma’aikata a jihar Benue sun karbi albashin su na wannan watan.

A cewar wasu daga cikin maaikatan da manema labarai suka zanta da su sun tabbatar da cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata suka fara samun albashin su na wannan watan.

Matakin rashin biyan albashin dai ya shafi tattalin arzikin jihar ta fuskoki da dama musamma ma masu kananan masanaantu da yan kasuwa yayin da dama daga cikin maaikatan su ka samu kansu cikin basussuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *