Bankin duniya ya bayyana goyon bayansa ga matakin cire tallafin man fetur

Bankin Duniya ya bayyana goyon bayansa ga matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na cire tallafin mai da kuma daidaita  farashin canji a kasuwannin canjin kudin kasashen ketare.

A yayin wani taro da Bankin Duniya ya shirya don yi nazari akan tattalin arzikin kasar nan cikin watanni shida da suka gabata a ranar Talata, Daraktan bankin anan Najeriya, Dokta Subham Chadhuri, ya bayyana cewa duk da cewa manufofin da gwamnatin ke dauka masu  tsauri ne, sai dai kuma sun zama wajibi a aiwatar dash idan har ana son kawo karshe koma-bayan sa ake samu akan tattalin arzikin.

Dokta Chadhuri ya bayyana cewa a halin yanzu kudaden da bankin duniyan ke bai wa Najeriya ya kai sama da dala biliyan goma, yana mai jaddada kudirin bankin na cigaba da  tallafawa sauye-sauyen tattalin arzikin kasar nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *