Tinubu ya umarci FAAN ta canza wa wasu filaye 15 zuwa sunan wasu fitattun ’yan Najeriya.

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta canza wa wasu filaye 15 zuwa sunan wasu fitattun ’yan Najeriya.

Daga cikin sunayen har da filin jirgin sama na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wanda aka saka wa sunan tsohon Shuagaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Umarnin dai na kunshe a cikin wata wasika da aka aike wa dukkan Shugabannin Gudanarwa na filayen jiragen, wacce ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta aike mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Yunin 2023.Wasikar na dauke ne da sa hannun Daraktar Kula da Filayen a Ma’aikatar, Misis Joke Olatunji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *