Mukaddashin babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan Olukayode Egbetokun, ya bayar da umarni ga dukkan ayarin ‘yan sanda da su bi duk ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa.
IG ya ba da umarnin ne a ranar Litinin yayin ganawarsa da tawagar ‘yan sanda ta musamman (Mobile Police Squadron) da kwamandoji a shedikwatar rundunar da ke Abuja.
A cewarsa, dole ne jami’an rundunar su yi koyi da doka idan har ana son a mutunta jama’a. Don haka ya yi alkawarin yin jagoranci ta hanyar da ta dace, tare da yin alkawarin kiyaye dukkan ka’idojin zirga-zirga.
Da yake karin haske, IG din ya kuma ce sabuwar tawagar da aka kirkira ta musamman (Special Intervention Squad) za ta kunshi kwararrun jami’ai 40,000, wadanda aka zabo daga rukunin jami’an ‘yan sanda na wayar tafi-da-gidanka da kuma dukkan sassan da ke cikin hukumar a fadin kasar.