Buhari ya dakatar da batun cire tallafin man fetur da kuma daidaita tsarin canjin kudin kasashen waje na kasar “zuwa lokacin da ya dace” – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban Muhammadu Buhari ya dakatar da batun cire tallafin man fetur da kuma daidaita tsarin canjin kudin kasashen waje na kasar “zuwa lokacin da ya dace.”

Shehu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, makwanni hudu bayan da Shugaba Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki daga hannun Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, ya kuma sanar da cire tallafin man fetur, inda farashi litar mai ta tashi daga naira 184 zuwa sama da naira 500.

Shehu ya kuma yi nuni da cewa idan za a yi maganar gaskiya a siyasance gwamnatin Buhari, a kwanakinta na karshe, ba za ta iya ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da ka iya girgiza kasa ba saboda jami’yyar APC na bukatan lashe zabe.

Mai magana da yawun tsohon shugaban ya ci gaba da cewa duk da cewa tsohon shugaban kasan bai cire tallafin man fetur ba, amma ya cire tallafin wutar lantarki da tallafin taki da tallafin kan aikin Hajji, da na ziyarar Jerusalem, da tallafin dizal, da na man jirgin sama, da tallafin kalanzir da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *