Wadanda aka samu da hannu a hatsarin kwale-kwalen da ya haifar da bacewar dalibai za su dandana kudarsu – Gwamnan Kuros Riba

Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba, ya ce wadanda aka samu da hannu a hatsarin kwale-kwalen da ya haifar da bacewar daliban likitanci a jihar, za su dandana kudarsu.

Gwamnan ya yi magana ne a daidai lokacin da yake ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin wanda wani jirgin ruwa mai saukar ungulu dauke da daliban likitanci 14 ya kife da misalin karfe 3 na rana, a Marina Resort dake babban birnin jihar.

Da yake magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Mista Emmanuel Ogbeche, Gwamna Otu ya fusata da cewa jirgin ya cika makil da wasu fasinjojin da ba a ba su rigar ceto ba.

A cewar rahotanni, uku daga cikin daliban sun bace har zuwa lokacin da rahoton ya bayyana, yayin da wasu 11 suka tsallake rijiya da baya, inda sojojin ruwan Najeriya da mutanen kauyen suka ceto su.

Daliban sun ziyarci wurin shakatawa na Marina ne a wani bangare na gudanar da bikin makon lafiya na shekara-shekara na kungiyar Daliban Likitanci ta Najeriya (NiMSA), kuma sun fito ne daga makarantu daban-daban na jihar. Bayan da ya tabbatar da cewa za a hukunta wasu mutanen da suka aikata laifin hatsarin kwale-kwale, gwamnan ya bukaci dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen gano mutanen uku da har yanzu ba a gansu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *