NiMet ta yi hasashen gajimare da tsawa daga yau Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen gajimare da tsawa daga yau Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.

Sakamakon yanayi na NiMet da aka fitar jiya Lahadi a Abuja ya yi hasashen yanayi mai hadari a yau Litinin da hasken rana jefi-jefi a yankin Arewa tare da yiwuwar tsawa da safe a sassan Taraba da Kebbi.

A cewar hukumar, ana iya samun tsawa a sassan jihohin Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Kaduna, Taraba, Kano, Katsina, Zamfara da Kebbi da yammacin wannan rana.

NiMet ya kuma yi hasashen tsawa da ruwan sama madaidaici a yawancin sassan yankin nan gaba da rana.

A cewar NiMet, ana sa ran yanayin rana tare da gajimare jefi jefi a yankin arewa da safiyar gobe Talata. Ta yi hasashen tsawa a wasu sassan Adamawa, Taraba da jihar Kaduna da yammacin ranar Talatar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *