Kamfanonin rarraba wuta sun tabbatar da shirinsu na karin harajin da masu amfani da wutar lantarkin ke biya a Najeriya

Kamfanonin rarraba wutar lantarki, sun tabbatar tare da dagewa kan shirinsu na karin harajin da masu amfani da wutar lantarkin ke biya a fadin kasar nan da zai fara daga ranar 1 ga watan Yulin 2023, duk da cewa kungiyar kwadago ta Najeriya ta nuna rashin gamsuwa da shirin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai kungiyoyin kwadago da kamfanonin rarraba wutar na Discos da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya suka yi karo da juna a kan shirin karin kudin wutar da masu amfani da wutar lantarkin ke biya a fadin kasar nan.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce “shirin kara kudin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 nan da ranar 1 ga watan Yuli, ya kasance rashin lissafi ne da nuna halin ko in kula ga walwalar masu amfani da wutar lantarki, musamman talakawa,” kuma ya yi gargadi game da matakin na Discos.

Sai dai a sanarwa daban-daban da suka aike ga abokan huldarsu kamfanonin na Discos sun sanar da cewa za a kara kudin wutar lantarki daga ranar 1 ga Yuli, 2023, kamar yadda suka bayar da dalilan hakan tun a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *