Gwamnan Sakkwato ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci ga gaba da zaman lafiya

Gwamnan Jihar Sakkwato Dokta Ahmed Aliyu Sokoto ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci ga gaba da zaman lafiya tare da kiyaye bin doka da oda.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa ya fitar dangane da farmakin da aka kai wa wani Usman Buda Mai Hanji da ake zargin ya yi kalaman batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. a babbar mayanka ta Sakkwato da safiyar Lahadi.

Gwamnan ya yi kashedi ga jama’ar jihar da su kiyeye duk wani yunkuri ko kalami da zai iya taba kima da darajar Manzon Allah, musamman ma dai a gari irin Sakkwato wanda gari ne na musulmai.

Gwamnan ya bayyana cewa mutanensa na da matukar soyayya da kauna ga Annabin Rahama ta yadda ba za su yi wasa da taba janibinsa ba, kan haka ya bukaci al’umma da su ci gaba da mutunta wannan kauna da suke yi.

Dokta Aliyu ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta taba daukar batun yin batanci ga fiyayyen halitta da sassauci ba, yana mai cewa za ta tabbatar an hukunta duk wanda aka kama da yin batanci ga fiyayyen halitta a bisa ga tanadin shari’ar musulunci.

Kazalika, ya ba da tabbaci cewa a shirye gwamnatinsa take don ganin ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *