Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabbin kwamishinoni da su kara wa harkokin mulki kimar da ba a taba samu ba

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin, ya bukaci sabbin kwamishinonin sa da aka rantsar da su kara wa harkokin mulki kimar da ba a taba samu ba.

Rahotanni na cewa Gwamna Abba ya bayya cewa su bada tallafin su ta hanyar bayar da gudummawa domin dawo da dukiyoyin Kano da aka salwantar.

Bayan haka, ya umarce su da su gaggauta komawa bakin aiki a ma’aikatun da aka tura su.

A wani gagarumin biki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Litinin don gudanar da walima Abba K Yusuf ya kalubalanci sabon babban Lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi, tare da wasu sabbin kwamishinonin, da su gaggauta daukar matakai domin ci gaban jihar cikin gaggawa.

Kazalika Yusuf ya bukace su da su sadaukar da kansu wajen gaskiya da rikon amana yayin gudanar da ayyukansu, kamar yadda jam’iyyar ta gabatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *