Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa na kokarin rage wa yan kasa
radadin cire tallafin man fetur.
Shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne yayin ganawarsa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa
da wasu kasashen turai da ke maƙwaftaka da Faransa.
Tinubu ya ce dole akwai buƙatar kuɗi domin aiwatar da shirin rage raɗaɗin Ya kuma bayyana hanyar da ya bi wajen shawo kan ƙungiyoyin kwadugo har suka fasa zanga- zangar da suka shirya.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa tuni aka kammala aikin lalubo hanyoyin rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗi da ƙuncin cire tallafin man fetur.
Tun a jawabin bikin rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Shugaban Kasa Tinubu ya sanar da cewa tallafin man fetur ya tafi domin acewarsa gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta ware kuɗin biyan tallafin ba a cikin ƙunshin kasafin kuɗin 2023.