Jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai biliyan $ 103.3

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai
Dalar Amurka biliyan 103.3, kwatankwacin Naira tiriliyan 49.8 ya zuwa ranar 21 ga watan Maris.
DMO ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ofishin ya ce bashin ya kuma hada da kudaden da ake bin Jihohi da Gwamnatin Tarayya, sai dai
adadin bai kunshi Naira tirliyan 22.7 din da CBN ke bin Gwamnatin Tarayya ba, wanda Majalisar
Dokoki ta Kasa ta sahale wa gwamntin ciyowa a watan Mayun 2023. Shi wancan adadin za a saka
shi a jerin basussuka na cikin gida daga watan Yunin 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *