Gwamnatin jihar Edo ta kara kudin makaranta na jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma, da fiye da
kaso 300.
Kungiyar daliban Najeriya Ta Kasa (NANS) ta caccaki gwamnatin jihar kan wannan mataki
da ta dauka.
Kungiyar daliban ta ce karin wani yunkuri ne na sanyawa ilimin jami’a ya fi karfin talakawa
Kungiyar daliban ta yi barazanar saka kafar wando daya da gwamnatin jihar idan har ba a yi wani abu don sake duba abun da ta bayyana a matsayin karin kudin makaranta na tashin hankali ba inda ta ce za ta nuna turjiya kan duk wani yunkuri na hana talakawa karatun jami’a a kasar nan.