Yayin da bikin Eid-el-Kabir da akafi sani da Babbar Sallah ke karato wa, masu sayar da shanu a cikin birnin Bauchi sun ce kasuwar ba ta bunkasa kamar yadda ake tsammani ba.
Abubakar Bura Adamu, dillalin shanu a wata kasuwar shanu ta zamani da ke kusa da tashar mai ta AY Makama, ya shaida wa Majiyar mu cewa mutane za su so su saya, amma ba za su iya yin hakan ba sai da kudi a hannunsu.
“Alhamdulillah kasuwanci na tafiya amma ba yadda aka saba ba” . “sabanin shekarun baya. Abokan ciniki suna siyan dabbobin amma ba yadda aka saba ba.”
Abubakar ya kara da cewa wasu daga cikin kwastomomin suna korafi kan farashin kuma sun yanke shawarar ba za su saya ba sai bayan biki ko kuma lokacin da farashin ya dan yi kasa kadan.
“A shekarun baya, da kyar aka bude daya don kasuwanci ba tare da sayar da shanu sama da biyar ba amma wannan shekarar ta sha bamban kuma kamar yadda nake magana da ku yanzu, babu daya daga cikinmu da ya sayar da ko daya,” inji shi.
Lamarin ya fi karfin tunani, in ji wani mai sayar da kayayyaki, Abubakar Abdulhamid, wanda ya bayyana cewa yanzu haka mutane kusan biyar ne ke bayar da kudi don sayen saniya guda.