Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama a rukunin gidaje na Trademore

Ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama a fitaccen rukunin gidaje na Trademore Estate
dake Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce ambaliyar ta lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon ruwan sama da aka yi
a safiyar ranar Juma’a.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa, ambaliyar
ruwan ta tafi da direban wata mota kirar Peugeot 406 a kan titin Imo dake cikin rukinin gidajen,
yayin da aka ceto wasu mutane 4 wadanda aka tabbatar cewa suna cikin koshin lafiya.

An ga mazauna yankin a lokacin da ake ruwan, suna kokarin ceton rayukansu da dukiyoyinsu
bayan da ruwan ya mamaye masu gidaje.

Rukunin gidajen Trademore ya shafe shekaru yana fama da munanan matsaloli na ambaliya
wanda ya haddasa rashin rayuka da kuma asarar dukiyoyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *