Gwamnan Kano ya biya bashin da NECO take bin jihar

Biyo bayan halin kuncin da ake fama da shi na cire tallafin man fetur, gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Yusuf ya amince da warware basussukan da hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO ta ke bin jihar

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta shafin sa na Twitter.

A cewarsa, an yanke shawarar ne don baiwa dalibai 55,000 na makarantun gwamnati damar zana jarabawar kammala makarantun sakandare SSCE na shekarar 2023.

“A wani bangare na kudirin gwamnatinmu na sake mayar da bangaren ilimi ta hanyar ba su damar shiga tsakani da ake bukata.

“Na amince da gaggauta daidaita kudaden da hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta ke bin jihar domin baiwa dalibai 55,000 na makarantun gwamnati damar shiga rubuta jarabawa SSCE 2023”. ya rubuta.

Mun ta tuna cewa a shekarar 2022 ne hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta sha alwashin hana daliban Kano rubuta jarabawar kan bashin da take bin jihar na tsabar kudi naira biliyan 1.5.

An shirya fara rubuta jarabawar NECO a ranar 27 ga watan Yuni 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *