FG ta amince da sabuwar doka da za ta bayar da dama ga gwamnatocin jihohi da samar da kuma rarraba wutar lantarki.

Gwamnatin tarayya ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta bayar da dama ga gwamnatocin jihohi da kuma daidaikun jama’a su samar da kuma rarraba wutar lantarki.

Kudurin dokar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya saka wa hannu a ranar 9 ga watan Yuni, na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya sama da mutum miliyan 200 ke fama da matsalar wutar lantarki.

Dakta Ibrahim Danbatta, masani kan harkar makamashi a Najeriya, ya ce wannan dokar za ta kawo sauyi kan harkokin lantarki.

Kafin lokacin da aka aiwatar da wannan sabuwar dokar, kamfanin rarraba wutar lantarki na TCN baki daya yana karkashin gwamnatin tarayyar Najeriya.

Sabuwar dokar ta kasance sakamakon sauye-sauyen da aka yi ta yi daga lokaci zuwa lokaci kan fannin
makamashi a kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afirka.

Kafin a samu wannan sauyin, dakon wutar lantarki da rarraba ta ya rataya ne a wuyan hukumar NEPA.
An dai shafe shekaru ana kokarin magance matsalar wutar lantarki a Nijeriya, sai dai kullum lamarin na kwan- gaba-kwan-baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *