Babban Bankin Nijeriya ya dage takunkumin ajiye kudi adadin Dala dubu goma asusun ajiya na kudaden waje a wani bangare na gyaran fuska kan harkokin Bankin.
Bankin ya ce, masu asusun suna da ‘yancin ziyartar asusunsu a kowanne lokaci ba tare da kayyadewa ba.
Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan wani taro da kwamitin
ma’aikatan bankuna a ranar Lahadi.
An yi taron ne don ba da kwarin guiwa ga masu asusun Dala, kan sauye-sauye da Babban Bankin ya yi a kasuwar ‘yan canji na baya-bayan nan da kuma tattaunawa da aiwatarwa da kuma tasirin sauye-sauyen manufofin ga abokan huldar bankuna.