An samu sabani tsakanin wasu cikinjagororin jam’iyyar APC sakamakon fafutukar samun kujerar Minista

Fafutukar samun kujerar Minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya janyo sabani tsakanin wasu cikin
jagororin jam’iyyar APC.

Rahotanni sun ce gwamnoni masu ci da tsofaffin gwamnonin jihohi da shugabannin APC su na ta kai kawo domin ganin shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ba su mukamin na Minista.

Baya ga wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, akwai kusoshin jam’iyyun adawa irinsu PDP da NNPP da ke harin Ministoci a gwamnatin mai-ci.

Wasu majiyoyi sun ce sabon shugaban kasar zai aika da sunayen Ministocinsa zuwa majalisa a ranar 4 ga Yuli da ‘yan majalisar dattawa za su koma bakin aikinsu.

Bayanai sun tabbatar da cewa za a rantsar da Ministoci ne bayan kammala shari’ar da ake yi a kotu a kan
sakamakon zaben shugaban kasa.

A jihohi irinsu Osun, rikici ake yi tsakanin tsohon Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da magajinsa Gboyega Oyetola da ya rasa tazarce a 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *