Sarkin Musulmi ya sanar da Litinin, 19 ga watan Yunin 2023 a matsayin 1 ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da Litinin, 19 ga watan Yunin 2023, a matsayin 1 ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya, sakamakon ganin jinjirin watan a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da Kwamitin ganin wata na mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya ya wallafa a shafinsa na
Twitter, ya ayyana ranar Laraba 28 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a gudanar da babbar salla a faɗin
Najeriya.

Sanarwar ta ambato mai alfarma Sarkin Musulmin Muhammad Sa’ad Abubakar lll na yi wa al’ummar
musulmin ƙasar fatan alkari da fatan yin sallah lafiya.

Tun da farko ita ma ƙasar Saudiyya ta bayyana ganin jinjirin watan na Zul-Hijjah, inda ta ayyana ranar talata 27 ga watan Yuni a matsayin ranar tsayuwar Arfa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *