Sanusi ya bayyana abin da ya tattauna da Tinubu bayan da ya kai masa ziyara

Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya bayyana abin da ya tattauna da Shugaban Kasa
Bola Tinubu bayan da ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Basaraken, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nigeria ne, ya ce yayin ganarwarsu ya gode
wa shugaban “dangane da alkiblar da ya dauka kan gyara tattalin arzikin kasar nan ciki har da
cire tallafin fetur da samar da farashin musayar dalar Amurka daya tal da sauransu.

Muhammadu Sanusi II ya gana da Shugaban Kasa Tinubu, kwanaki kadan bayan an cire mutumin da
ya gaje shi a shugabancin CBN, Godwin Emefiele, daga kan kujerarsa sannan aka kaddamar da bincike a kan ofishinsa.

A karshe ya ce ya bai wa sabon shugaban tabbaci cewa a ko da yaushe a shirye yake ya ba da
shawara idan bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *